Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kano: An Tsige Kanin Ganduje Daga Saurata


Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II

Rahotanni daga Jihar Kano na cewa Majalisar masauratar Jihar ta warware rawanin hakimin Ganduje, Alhaji Sani Umar Ganduje.

Shi dai Alhaji Umar kani ne ga gwamnan jihar mai ci a yanzu Abdullahi Umar Ganduje.

Rahotanni sun ce an cire shi ne bisa wata takaddamar kudade da ke tsakaninsa da wasu talakawan da ke yankin.

A daya bangaren kuma masarautar garin Dutse da ke Jihar Jigawa ita ma ta dakatar da hakimin Gundumar Bamaina, Alhaji Mustapha Sule Lamido daga aikinsa.

An dakatar da shi ne saboda shari’ar da ke tsakaninsa da hukumar EFCC a babbar kotu da ke Abuja.

Saurari wannan rahoto na Mahmud Ibrahim Kwari domin jin karin bayani, ciki har da tsokaci da masana shari’a suka yi dangane da wadannan matakan:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:20 0:00
Shiga Kai Tsaye


Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG