Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Maharan Boko Haram Sun Kashe Akalla Mutane 50 A Kauyen Dolari


A man walks past burnt out houses following an attack by Boko Haram in Dalori village 5 kilometers (3 miles) from Maiduguri, Nigeria, Jan. 31, 2016.
A man walks past burnt out houses following an attack by Boko Haram in Dalori village 5 kilometers (3 miles) from Maiduguri, Nigeria, Jan. 31, 2016.

‘Yan Boko Haram sun kai hari a wani kauye inda suka kashe akalla mutane 50. Shaidun gani da ido sun bayyana cewa, ‘yan ta’addar sun dirarwa kauyen Dolari da daddaren ranar Asabar suka dinga harbin jama’a tare da kona gidaje.

Wani soja ya fadawa kamfanin dillancin labaran AP cewa wasu mata guda 3 ‘yan kunar bakin wake sun tada kansu cikin taron jama’a suka jikkata da dama daga cikinsu.

A yayi da su kuma kungiyar rajin kare ‘yancin bil’adama ta Amnesty International ke dada matsa lamba akan yin binciken lamarin soji.

Sun ce ya kamata a binciki gagororin sojin da ake zargin da wulakantar da gwamnatin Najeriya da laifukan yaki sakamakon rikon sakainar kashin da suka yi ya ja rasa rayukan jama’a.

XS
SM
MD
LG