Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

KANO: Jami'an Tsaro Sun Yi Wa Masallacin Ashabul Khafi Kawanya


Sheikh AbdulJabbar Nasiru Kabara

Jami’an tsaro a Kano sun yi kawanya a masallacin Ashabul Khafi dake Unguwar Gwale a cikin birnin Kano, wurin da Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ke gudanar da karatu.

Hakan na zuwa ne kasa da sa’o’I 24 da umarnin gwamnatin jihar Kano wadda ke haramtawa Malamin gudanar da wa’azi karantarwar a wurin da-ma kowane wuri a fadin jihar saboda zarginsa da kalaman tunzura Jama’a da ka iya barazana ga zaman lafiya a jihar.

A cikin wata sanarwa, kwamishinan labarun gwamnatin Kanon, Comrade Mohammed Garba yace, majalisar zartarwa jihar ta kuma umarci kafofin yada labarai a fadin jihar su daina saka muryar Malamin a dukkanin shirye shiryen su domin tabbatar da doka da oda a tsakanin al’umar jihar.

Sheikh AbdulJabbar Nasiru Kabara yana wa'azi a Masallaci
Sheikh AbdulJabbar Nasiru Kabara yana wa'azi a Masallaci

Bayanai daga majiyoyin tsaro a Kano na nuni da cewa, Sheikh Abduljabbar din ya yi wata ganawa da makusanta da almajiran sa game da yanayin da aka tsinci kai. Sai dai babu wani bayani dangane da sakamakon tattaunawar ta su.

takaddama-tsakanin-kungiyoyi-da-gwamnatin-jihar-kano-kan-wuraren-ibada

shawarar-ganduje-kan-makiyaya-ta-saba-doka-bulama-bukarti

A hannu guda kuma, wasu mabiya darikar shi’a sun gudanar da wata kwarkwaryar zanga zanga domin nuna goyon bayan su ga Malamin. Sai dai cikin sauri ‘yan sanda suka tarwatsa masu zanga zangar jim kadan bayan sun fara yin gangami a kusa da asibitin Murtala dake cikin birnin Kano.

Yanzu haka dai gwamnatin jihar ta kafa kwamitin bincike kan yadda Malamin ke gudanar da harkokin sa. Kwamitin dai ya kunshi Jami’an tsaro da Malamai da kuma Jami’an gwamnati. Ana sa ran rahotan kwamitin ne zai baiwa gwamnati alkibilar mataki na gaba game da wannan batu.

Masallacin Sheikh AbdulJabbar Nasiru Kabara
Masallacin Sheikh AbdulJabbar Nasiru Kabara

A martanin sa ga matakin na gwamnati, Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ya alakanta lamarin da cewa, siyasa ce kawai, domin kuwa a cewarsa,yana cikin wadanda ba su goyi bayan gwamnatin Abudllahi Umar Ganduje ba. A don haka sai ya bukace almajiran sa da sauran mabiya da su dauki damarar zabar gwamnatin da zata ba su sukunin gudanar da addininsu yadda ya kamata a nan gaba.

Wannan lamarin ya ja hankalin wadansu masu sharhi a shafukan zumunta

Wakilinmu dake Kano ya ruwaito cewa, Jama’a a birni da kewayan Kano na ci gaba da gudanar da harkokin su na yau da kullum yadda ya kamata.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG