Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Karawar Villareal, Juventus A Gasar UEFA


'Yan wasan Villareal suna atisaye
'Yan wasan Villareal suna atisaye

Kocin kungiyar Unai Emery zai yi Rashin dan wasa Gerard Moreno, amma kuma zai iya dogaro da Arnaut Danjuma, wanda ya zura kwallaye 8 a gasar La Liga a wannan kakar wasa.

‘Yan wasan Villareal na shirin karawa da abokanan hamayyarsu na Juventus a gasar cin zakarun nahiyar turai na UEFA Champions League.

Wannan shi ne karon farko cikin shekaru 13 da ‘yan wasan na Villareal da ake wa lakabi da “Yellow Submarine” za su buga a zagayen ‘yan 16 a gasar ta UEFA.

Wannna wasa nasu na zuwa ne bayan nasarori hudu da suka samu a jeri a gasa daban-daban da suka buga a baya-bayan nan.

Kocin kungiyar Unai Emery zai yi Rashin dan wasa Gerard Moreno, amma kuma zai iya dogaro da Arnaut Danjuma, wanda ya zura kwallaye 8 a gasar La Liga a wannan kakar wasa.

Ita ma Juventus na da nata ‘yan wasan da ba za su buga, wadanda suka hada da kyaftin Giorgino Chiellini, Paulo Dybala da Federico Bernadeschi wadand duk suke fama da jinya.

Sako: Wannan labari ne daga kamfanin dillancin labarai na AP da Mahmud Lalo ya fassara.

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG