Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar Algeria Na Ci Gaba Da Jibge Bakin Haure a Nijar


Shugaban Nijar Niger Mahamadou Issoufou

Duk da kashedin da kasar Nijar ta yi mata akan jibge mata bakin haure, har yanzu Algeria na cigaba da yin hakan musamman a cikin jihar Agadez

Duk da gargadin da kasar Nijar ta yiwa kasar Algeria akan ta daina jibge mata bakin haure daga wasu kasashen Afirka, har yanzu ta ci gaba da yin hakan.

Kwana kwanan nan kasar Algeria ta sake jibge wasu ‘yan asalin Afirka da suka hada da wata ‘yar kasar Kamaru a kasar Nijar din. Wanna ‘yar Kamaru din ta bayyana irin mugun halin da suka shiga a hannun Larabawan Algeria.

A cewar ta daga cikin gidansu aka kwashesu, bayan da suka sace kayan su aka tasa keyarsu. Sun ce Larabawan da ke tare da su, suna fada masu cewa su Larabawa ba daya suke da bakake ba.

‘Yan Nijar na ci gaba da tsokaci akan wannan lamarin. Habibu Mummuni wani dan kungiyar farin hula mai fafutikar kare mutuncin ‘yan kasa y ace Jamhuriyar Nijar tana da gaskiya akan hana jibge mata bakin haure. A cewarsa ba’a san yadda mutanen da ake jibgewa a kasar suke ba. Akwai na kwarai akwai kuma mugga. Kasar nada gaskiya ta dauki matakan kare hakkin ‘yan kasarta.

Yace akwai dokoki akan bakin haure. Kamata ya yi Algeria ta mayar da kowane bakin haure kasarsa saboda haka kasar Turkiya ta yi.

Ga rahoton Haruna Mamman Bako da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:55 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG