Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar Benin Ta Rufe Mashigar Kogi Da Nijar A Wani Takaddamar Kasuwanci


Le long de la rivière de Niamey, le 21 décembre 2017.
Le long de la rivière de Niamey, le 21 décembre 2017.

Kasar Benin ta toshe mashigar kan iyaka da Nijar ta ratsa tsakanin makwabta, kamar yadda majiyoyi suka shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa a ranar Alhamis, a wani tashin hankali da ya barke tun bayan da sojoji suka kwace mulki a Yamai a watan Yulin da ya gabata.

A cikin 'yan makonnin nan dai kasashen Benin da Nijar su ka ci gaba da kara zarge-zargen na safarar kayayyaki, duk da cewa kungiyar ECOWAS ta yammacin Afirka a watan Fabrairun da ya gabata ta dage takunkumin da ta kakaba wa shugabannin sojin Nijar.

Yan kasuwa masu neman tsallaka kogi
Yan kasuwa masu neman tsallaka kogi

Dangantaka a kan iyakar kuma tana da sarkakiya sakamakon bullar aika-aikan mayakan IS a Nijar da Burkina Faso da ke kara yin barazana ga Benin da makwabciyarta Guinea, Ghana da Togo.

Tun farko kasar Benin ta sanar da bude kan iyakarta a daidai lokacin da kungiyar ECOWAS ta dage takunkumin.

Sai dai iyakar ta ci gaba da kasancewa a rufe a bangaren Nijar, lamarin da ya harzuka shugaban kasar Benin Patrice Talon, wanda ya ce Nijar ta dauke su ne tamkar a matsayin makiyi.

Patrice Talon
Patrice Talon

A cewar wani jami’in sojan kasar Benin a Malanville, dan sanda da ke aiki a yankin da kuma mazauna yankin da suka zanta da kamfanin dillancin labaran Faransa AFP, gadar Malanville da ke samar da mashigar kan iyaka tsakanin kasashen biyu na zaune a rufe a bangaren Nijar, kuma har ila yau, an haramta jigilar kayayyaki a kogin Nijar.

Wasu mazauna Malanville da dama sun shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa sojojin Nijar sun tarwatsa su a daya bangaren don haka ba za su iya tsallake kogin ba.

Rufe zirga-zirgar kogin shi ne na baya-bayan nan a jerin shawarwarin da suka shafi kasuwanci tsakanin kasashen biyu.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG