Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar Gambia Ta Fice Daga Kotun Duniya Ta Kasa Da Kasa ICC


Shugaban Gambia Yahya Jammeh a shugabannin ECOWAS a taronsu a Abuja, Disamba 16, 2015.

Kasar Gambia ta zargi kotun bin bahasin laifuka ta duniya da laifin cewa tana juya bayanta ga “laifukkan yake-yake” da ake aikatawa. Kasar ta gambia tana wannan kalamin ne yayinda ita ma take ficewa daga kotun, watau ta bi sahun kasashe irinsu Afrika ta Kudu da Burundi, wadanda su ma a farkon watan nan suka janye kansu daga kotun.

Haka kuma ministan watsa labaran Gambia, Sheriff Bojang ya zargi kotun da nuna wariyar launin fata da kuma rashin yi wa kasashen Afrika adalci.

Yace koda yake ana kiran kotun “Kotun Kasa da kasa” kotun Turawa ce kawai da kullum take kuntatawa mutanen da ba Turawan ba, musamman mutanen Afrika.

Kusan dukkan shara’oi 10 da wannan kotun ta gudanar, in bayan guda daya tak, sun shafi kasashen Afrika ne.

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG