Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar Iran tana yiwa kasashen yankin Gulf barazana - John Kerry


John Kerry sakataren harkokin wajen Amurka da wasu shugabnnin kasashen yankin Gulf

Amurka da abokan kawancenta na gabar tekun yankin Gulf suna da damuwa daya game da ayyukan Iran dake tada zaune tsaye a yankin, inji sakataren ma’aikatar harkokin wajen Amurka John Kerry jiya alhamis, bayan tattaunawa da ministocin kungiyar hadin kan majalisar kasashen yankin Gulf-GCC.

Zamu ci gaba da nuna dagewa kan irin wadannan takalar, inji Kerry yayin wata ganawa da takwaransa na kasar Saudiya Adel al-Jubeir.

Ya bayyana haka ne bayan tattaunawa kan harkokin tsaro a yankin da jami'an Bahran da kuma na kungiyar GCC.

Da yake magana a madadin kungiyar GCC da ta kunshi kasashe shida, Jubeir yace, idan Iran tana so ta daidaita dangantakarta da sauran kasashen, tilas ne ta sake tsare tsarenta.

Tun daga watan Satumba, jiragen ruwan soji suke ta kama jiragen dakon kaya dauke da makamai da aka hakikanta sun fito daga Iran ne. An hakikanta cewa, za a kaiwa ‘yan tawayen Houthi ne a Yemen.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG