Accessibility links

Kasashe Biyu Sun Ce Zasu Ba Edward Snowden Mafaka

  • Grace Alheri Abdu

Hoton Edward Snowden

Kasashen Venezuela da Nicaragua sun ce zasu ba mutumin da ya fallasa ayyukan sirrin Amurka,Edward Snowden mafaka.

Kasashen Latin Amurka biyu sun amince, su bada mafaka ga tsohon dan kwangilar cibiyar ayyukan tsaron Amurka ta hanyar na’ura Edward Snowden wanda Amurka ke nema sabili da fallasa ayyukanta na sa ido.

Shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro ya fada jiya jumma’a cewa, ya tsaida shawarar ba Snowden mafaka bisa dalilan jinkai domin kare shi daga tuhuma a Amurka.
Jiya jumma’a har wa yau, shugaban kasar Nicaragua Daniel Ortega yace zai ba Snowden mafakar siyasa idan ya yiwu.

Babu tabbacin yadda Snowden zai iya shiga jirgi zuwa kasashen. Ana kyautata zaton yana makale a bangaren yada zango na tashar jirgin saman kasar Moscow kuma ya kasa fita domin bashi da takardun tafiya.

Snowden ya nemi mafaka a kasashe da dama. Sai dai Amurka tana so a tasa keyarshi sabili da fallasa cewa, cibiyar tsaron kasar Amurka tana satar sauraron wayar tarhon Amurkawa.

Cibiyar ta NSA ta bayyana cewa, bayanan da ta samu ta wannan hanyar sun taimaka wajen dakile yunkurin kai harin ta’addanci. Snowden yace yana so Amurkawa su sani cewa, gwamnatinsu tana sa masu ido.
XS
SM
MD
LG