Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasashen Afirka Sun Amince Su Fice daga Kotun Manyan Laifuka Na Kasa da Kasa


Shugabannin Afrika a taron AU da suka yi a hedkwatarsu dake Addis Ababa kasar Habasha
Shugabannin Afrika a taron AU da suka yi a hedkwatarsu dake Addis Ababa kasar Habasha

Kungiyar Tarayyar Afirka na cigaba da, abin da ta kira, "janyewa na sannu a hankali" daga Kotun Manyan Laifuka Ta Duniya, matakin da zai yi tasiri kan zaman lafiya da tsaro da kuma batun adalci a nahiyar.

Shugabannin kasashe da dama, wadanda da dama daga cikinsu, au ana zarginsu da aikata laifukan yaki, au Kotun Manyan Laifuka Ta Duniyar na nemansusun rattaba hannu kan wannan matakin ranar Talata a sadade, rana ta karshe a babban taron AU a Addis Ababa.

Yawancin lokaci Shugabannin Afirka kan zargi Kotun Duniyar da auna su ba bisa ka'ida ba, su na nuni da yadda cikin mutane 39 da kotun, mai mazauni a birnin Hague, ta tuhuma, 39 wato dukkansu kenan, 'yan Afirka ne.

Ba a yi wata babbar sanarwa ba kan wannan shawarar kuma Shugabannin kasashen sun yi saurin rufe taron, su na ta jinjina ma juna yayin da wani rukunin mawaka ke ta raira wakar taken kungiyar ta AU, wanda ya hada da hurucin nan mai cewa: "Bari mu dukufa wajen fafatuka tare, saboda dorewar zaman lafiya da adalci a duniya"

Majiyoyi biyu masu alaka da kungiyar ta AU sun tabbatar ma Muryar Amurka cewa an yanke wannan shawarar.

To saidai, a takaice, majiyoyin sun ce shawarar ba wajiba ba ce, kawai nuna goyon bayan AU ne a siyasance cewa duk lokacin da duk wata daga cikin kasashen Afirka 34 mambobin AU ke son ficewa daga Kotun, AU za ta goyi bayanta.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG