Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasashen Da Za Su Je Gasar Cin Kofin Duniya A Qatar


Kasar Qatar da za ta karbi bakuncin gasar cin kofin duniya
Kasar Qatar da za ta karbi bakuncin gasar cin kofin duniya

Ya zuwa yanzu an tantance kasashen da za su halarci gasar cin kofin duniya da kasar za ta karbi bakunci a watan Nuwamban bana.

Kasashen sun hada da Argentina, Brazil, Ingila, Faransa, Sifaniya da Belgium.

Har ila yau akwai Portugal, Jamus, Netherlands, Croatia, Denmark, Mexico da kuma kasar Amurka.

Sauran su ne, kasar Senegal, da Wales, Poland, da Austaraliya, Japan, Morocco, Switzerland, Ghana da kuma Hadaddiyar Kasar Koreya.

Sai kasar Kamaru, Sabiya, Canada, Costa Rica, Tunisiya, Saudi Arabia, Iran, da Kasar Ecaudor da masu masaukin baki kasar Qatar.

Har yanzu dai, kan batun shirin wasan kwallon kafa na Duniya na shekara ta 2022, Kocin Ingila, Gareth South Gate, ya gargadi , Marcus Rashford, da kuma Jadon Sancho, cewa akwai yiwuwar sunansu ba zai kasance cikin tawagar din Ingila ba, na gasar cin kofin duniya ta 2022.

Ya shaida musu cewa, suka ra zagewa sosai muddin suna son su kasance cikin ‘yan wasan da za su taka leda wa kasar Ingila a gasar kwallon kafa na duniya da za a gudanar a kasar ta Qatar.

Sai kuma batun abin kunyan da ya faru a hukumar kwallon kafa ta Duniya FIFA, inda tsohon shugaban, Michel Platini, ya bayyana cewa, lalle kan an shirya magudi, a gasar kwallon kafa ta Duniya a shekarar, 1998, inda ya ce ya yi katsalandan, wajen tsara yadda tima-timai za su kara da juna, ta hanyar tabbatar da cewa, kasar Faransa da kasar Barazil sun hadu a wasan karshe.

Faransa wacce ita ce ta dauki bakoncin gasar, sun fafata da kasar Barazil, wanda kuma daga karshe Faransa ce ta yi nasarar lashe kofin.

Ahalin da ake ciki, Michel Platini, yana fuskantar sharia’a tare da tsohon shugaban hukumar FIFA, Sepp Blatter, kan batun rashawa da cin hanci.

Saurari cikakken rahoton Abdulwahab Muhammad daga Bauchi:

Kasashen Da Za Su Je Gasar Cin Kofin Duniya A Qatar - 3'50"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:50 0:00

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG