Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasashen Duniya Na Bikin Tunawa Da Ranar Yaki Da Cutar Amosani-Sickle Cell


.
.

Kasashen duniya sun yi bukin tunawa da ranar yaki da cutar amosanin jini, daya daga cikin cututukan da suka fi wahalar da jama’a a kasashe masu tasowa.

NIAMEY, NIGER - An fi samu cutar ne a kasashe masu tasowa sakamakon karancin asibitoci da tsadar magunguna duk kuwa da cewa gwamnatoci da masu hannu da shuni na kasa da kasa na iya bakin kokarinsu wajen daukar dawainiyar masu fama da wannan cuta.

Ranar yaki da cutar amosanin jini wani lokaci ne na fadakarwa da kuma tayar da gwamnatoci da kungiyoyi daga barci game da nauyin da ke rataye a wuyansu a kokarin cimma nasarar wannan yaki na ceton rayuwa musamman a kasashe masu tasowa inda matsalar ta fi kamari.

A hirar ta da Muryar Amurka, Dr Foureratou Issoufou shugabar cibiyar kula da masu fama da cutar amosanin jini dake birnin Yamai ta ce matsalar cutar da na girma a kasar Nijar.

A albarkacin wannan rana ta 19 ga watan Yuni cibiyar kula da masu fama da wannan cuta ta shirya wani gangami a birnin Yamai domin neman gudumuwar jini daga wajen jama’a yayin da a wani bangare taron ya kasance wani lokaci na gwajin jini ga mutanen dake bukatar sanin ko suna dauke da kwayar cutar kokuma akasin haka.

Saurari rahoto cikin sauti daga Souley Moumouni Barma:

Kasashen Duniya Na Bikin Tunawa Da Ranar Yaki Da Cutar Amosani-Sickle Cell
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:33 0:00

XS
SM
MD
LG