Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Masana Kimiyi Na Yunkurin Samar Da Rigakafin Covid Na Feshin Hanci Maimakon Hanu


Ana ci gaba da haɓaka allurar rigakafin COVID-19 a matsayin feshin hanci maimakon alluran hanu aƙalla dakin gwaje-gwaje tara da kamfanoni a duniya, a cewar Hukumar Lafiya ta Duniya.

Banda cewa akwai rashin jin daɗin sukan allura a hannu, waɗannan alluran kuma na iya yin aiki mafi kyau fiye da allurar da ake ba wa hanu wajen dakatar da coronavirus inda ya fara shiga jiki.

Kuma ta hanyar kiyaye kwayar cutar daga yaduwa a cikin hancinmu da makogwaronmu, rigakafin feshin hanci yana iya yin kyakkyawan aiki na hana yaduwa daga mutum zuwa mutum. Wannan yana da mahimmanci musamman tare da nau’in omicron, wanda ke da saurin yaduwa.

Yawancin waɗannan alluran rigakafin na cikin gwaji na farko, don haka ba a bayyana lokacin da za’a samar da su ba. A halin yanzu daya daga cikin masu gwaje-gwajen sun fita daga gwajin, amma masana kimiyya a Amurka, China, Cuba, Iran da sauran wurare sun ci gaba.

Yayin da alluran rigakafin COVID-19 na yanzu na aiki wajen gina kariya , amma ya gaza wajen kariyar hanci da makogwaro.

Allurar rigakafin da aka fesa a cikin hanci zai yaƙa ƙwayar cutar da zaran yayi karo da shi.

Diamond da abokan aiki sun haɓaka maganin COVID-19 na feshin hanci kuma sun ba shi lasisi ga kamfanin harhada magunguna na Indiya Bharat Biotech.

Gaskiyar lamarin shine cewa allurar rigakafi ba ta samar da rigakafi mai yawa na hanci wannan shi ne dalilin da yasa cututtuka kamar nau’in omicron suna yaduwa sosaiduk da cewa harbuwar sa baya zuwa da tsanani.

Matukar dai hanci da makogwaronmu na dauke da kwayar cutar, za mu iya yada ta nan da nan, ko da ma ba mu san mun kamu da cutar ba. Wannan shine babbar matsalaa COVID-19.

Ingantacciyar maganin rigakafin fechin hanci zai iya taimakawa wajen magance shi, in ji Ursula Buchholz, shugabar sashin ƙwayoyin cuta na RNA a Cibiyar Kula da Cututtuka (NIAID).

XS
SM
MD
LG