Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasashen G5 Sahel Sun Dukufa Wajen Kawar Da Ta'addanci a Yankin


Taron Shuwagabannin G5 Sahel

Shuwagabannin kasashen G5 Sahel sun kammala taronsu na shekara shekara a jiya Talata a garin N’Djamena, inda suka tattauna hanyoyin da za su bullo wa kungiyoyin ta’addancin da suka addabi al’ummomin iyakokin kasashen Mali, Nijar da Burkina Faso.

Bayan tattaunawar ta tsawon kwanaki 2 taron na shugabanin kasashen G5 Sahel ya sake jaddada aniyar ci gaba da yakin da aka shafe shekaru 8 ana kafsawa da nufin murkushe kungiyoyin ta’addanci a yankin sahel.

Shugaban kasar Chadi Idriss Debi mai masaukin baki ya kudiri aniyar aika wasu Karin dakaru zuwa iyakokin Mali, Niger da Burkina Faso lamarin da tuni ya fara daukan hankalin masu sharhi kan sha’anin tsaro.

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa, wanda ya halarci taron ta hanyar bidiyo, ya ce rundunar sojan Barkhane za ta ci gaba da aikin tsaro a wannan yanki kafin nan gaba a dubi hanyoyin janye wani rukuni na wadannan askarawa kimanin 5100 sannu a hankali.

To sai dai wani mamba a kwamitin ‘yan majalisar dokokin kasashen G5 Sahel bugu da kari mamba a kwamitin tsaro a majalisar dokokin jamhuriyar Nijar, Honorable Hama Assa na ganin lokaci ya yi da MDD za ta sakar wa kasashen yankin sahel hurumin gudanar da wannan yaki kamar yadda aka sha nuna bukata a can baya.

A shekarar 2013 ne kasar Faransa ta girke sojoji a Mali da zummar murkushe ‘yan ta’addan da suka tare a Arewacin kasar kafin daga bisani wasu kasashen Yammacin duniya su shiga wannan yaki da sunan dauki ga sojojin kasashen yankin na sahel sai dai shekaru 8 bayan kaddamar da wannan yaki alamu na nuna abin na kokarin gagarar kundila. Koda yake wata majiya na cewa kungiyoyin ta’addancin wannan yanki sun fara kaura zuwa gabar tekun Guinea da Senegal.

Saurari rahoton cikin sauti daga Souley Moumouni Barma:

Kasashen G5 Sahel Sun Dukufa Wajen Kawar Da Ta'addanci a Yankin
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00


Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Gobara A Jihar New York

An Yi Jana'izar Mutane 15 Da Suka Mutu A Gobara A Jihar New York
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG