Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasashen Musulmi Sun yi Allah Wadai da Shawara Trump a Kan Birnin Kudus


Taron Kasashe Masu Yawan Musulmi
Taron Kasashe Masu Yawan Musulmi

Kasashe masu yawan al’umman Musulmi sun yi wani taro a jiya Laraba a Istanbul, kasar Turkiya kuma suka yi Allah wadai da shawarar da shugaban Amurka Donald Trump ya yanke na daukar birnin Kudus a matsayin babban birnin Isra’ila ya sabawa doka.

Taron na zuwa yayin da ake fama da rashin zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya tare kuma da ci gaba da yin tofin Allah tsine a kan batun birnin Kudus.


Shugaban Falasdinu Mahmoud Abbas da Sarkin Jordan Abdullahi na biyu, da shugaban Azerbaijan Ilham Aljey da shugaban Bangladesh Abdoul Hamid da kuma shugaban Iran Hassan Rouhani suna cikin shugaban kasashe da gwamnatoci 22 da suka halarci taron.

Kasashen Masar da Saudiya tare da wasu kasashe 23 sun aike da wakilan su.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG