Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasashen Turai Basu Cimma Matsaya Ba Akan 'Yan Gudun Hijira


'Yan gudun hijira kan iyaka tsakanin Austria da Hangary

Ministocin cikin gidan kasashen tarayyar Turai sun kasa samu daidaito game da maganar rarraba ‘yan gudun hijira 120,000 don tsugunar da su a tsakanin kasashensu.

Mafi yawancin Ministocin sun yarda da tsarin na rarraba ‘yan gudun hijiran, a yayin da yawancin botsarewa hakan ya bullo daga mafi yawancin kasashen Gabashin Turai ciki har da Hungary da Slovakia.

Wanda yawanci kan iyakokinsu ne mashigar farko ta ‘yan gudun hijiran masu son kutsawa Yammacin Turai da nufin samun sabuwar rayuwa da kuma gujewa yakin da yake daukar rayuka a Gabas ta tsakiya.

Yawancin shugabannin kasashen Turai sun koka da kasar Jamus da ta fito karara ta yi maraba da ‘yan gudun hijiran da yakin ya wartako daga kasashen Syria da wasu wurare na daban.

Jamus ta fusata game da yin kasa a gwuiwar takwarorinta na Turai wajen karbar bakuncin wadannan masu neman mafaka daga bala’in yaki.

A duku-dukun Litinin din jiya ne kasar Hungary ta datse kan iyakarta da kakkaifar waya tare da jibge ‘yan sanda da sojoji, don yin gadin digar jirgin kasa din da ‘yan gudun hijiran kan haura zuwa cikin kasar.

Suma kan iyakar Slovakia sun kara yawan shingayen tsaron kan iyakokinsu don dakile kwararar bakin. Fiye dai da ‘yan gudun hijira 430,000 ne ke neman mafaka a Turai da nufin tserewa masifar yakin ta’addanci a Syria da Iraki.

XS
SM
MD
LG