Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kashedin Amurka Ga Sauran Duniya Akan Makaman Nukiliyar Iran


Kasar Amurka na jan hankalin kasashen duniya akan wani yunkuri da kasar Iran keyi, na shirinta da zai bata damar kara yawaitar makaman kare dangi.

Amurka na jan hankalin kasashen Larabawa da sauran duniya da suyi taka tsan-tsan da barazanar Iran, akan kera makaman kared-angi, idan ba haka ba matsalar zata wuce haka.

Dalilin da yasa Amurka tayi wannan kiran shine, ranar Alhamis, an gano wasu makaman kare dangi da suka hada da Roka, jirage masu tuka kansu Drones, a kusa da Iran cikin Teku.

Wadannan makaman da muke bayyanar da su, suna nuni da cewar Iran a shirye take ta taimaka wajen dai-daita yankin.

Mai wakiltar Amurka na musamman a Iran Brian Hook, ya shaidawa manema labarai lokacin da yake tsaye a gaban wani Makamin kare dangi da Iran take kerawa, da sojojin Saudiyya suka kama.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG