Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

KASUWA A KAI MAKI DOLE: Hada-Hadar Kasuwanci A Kasuwar Panteka Da Ke Kaduna, Satumba 11, 2022


Yayin da ake hada-hadar sayen kayen masarufi a wata kasuwa a Kano
Yayin da ake hada-hadar sayen kayen masarufi a wata kasuwa a Kano

Shirin a kasuwa a kai maki dole na wannan makon ya kai ziyara kasuwar Panteka dake garin Kaduna.

WASHINGTON, DC - Wakilin Muryar Amurka Isah Lawal Ikara ya leka kasuwar Panteka sabuwa a garin Kaduna, inda ake saida tayoyin mota, gilashin mota da sauran sassan mota.

A gefe guda kuma akwai masu gyaran gilashin mota da kwalliyar mota. A hirarsa da wasu ‘yan kasuwar, sun bayyana cewa a lokacin damina suka fi ciniki sun kuma ce sana’arsu na tattare da hadari saboda wasu lokutan gilasan na fashewa.

‘Yan kasuwar sun kuma ce hauhawar farashin kayayyaki sakamakon annobar coronavirus ya shafi harkokin kasuwancinsu sosai. Hakazalika, matsalar tsaro na daga cikin kalubalen da ‘yan kasuwar ke fuskanta saboda yanzu masu zuwa sayayya daga jihohi makwabta ba su cika zuwa ba.

Saurari cikakken shirin cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:10:11 0:00
XS
SM
MD
LG