Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

DUNIYAR AMURKA: Martanin Amurka Bayan Da Isra'ila Ta Ce Sojojinta Ne Suka Kashe Shireen Abu Akleh Bisa Kuskure - Satumba 09, 2022


Mahmud Lalo
Mahmud Lalo

A ranar Litinin din da ta gabata, Ma’aikatar Tsaron Isra’ila ta fitar da wata sanarwa inda ta ce “mai yiwuwa," sojojinta ne suka harbe Abu Akleh bisa kuskure, a lokacin da suke musayar wuta da wasu Falasdinawa masu dauke da bindiga.

Ma’aikatar harkokin wajen Amurka, ta maida martani kan wata sanarwa da Isra’ila ta fitar kan kisan ‘yar jaridar nan Ba’amurkiya ‘yar asalin Falasdinu Shireen Abu Akleh a watan Mayu, inda ma’aikatar ta ce, Amurka za ta tursasa Isra’ilan ta sake duba matakan da sojojinta ke bi idan suna bakin aiki a Yammaci Gabar Kogin Jordan domin ganin an rage hadarin da ‘yan jarida da fararen hula ke fadawa. A yi sauraro lafiya:

DUNIYAR AMURKA: Martanin Amurka Bayan Da Isra'ila Ta Ce Dakarunta Ne Suka Kashe Shireen Abu Akleh Bisa Kuskure - 7'06" .mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:07:06 0:00

XS
SM
MD
LG