Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

KASUWA A KAI MAKI DOLE: Kalubalen Kasuwanci A Kasuwar Kayan Gwari Ta Jihar Imo, Satumba 18, 2022


Yayin da ake hadahadar sayen kayen masarufi a wata kasuwa a Kano
Yayin da ake hadahadar sayen kayen masarufi a wata kasuwa a Kano

Shirin Kasuwa a kai maki dole na wannan makon ya ziyarci kasuwar kayan gwari, da ke jihar Imo a kudu maso gabashin Najeriya.

WASHINGTON, DC - A watannin baya-bayan nan jihar Imo da ke kudu maso gabashin Najeriya ta fuskanci tashin hankalin ‘yan bindiga masu kisa da garkuwa da mutane don neman kudin fansa, lamarin da ya jefa al’umar yankin cikin yanayin zullumi.

Wakilin Muryar Amurka Lamido Abubakar, ya tattauna da wasu ‘yan kasuwar da suka bayyana cewa babban kalubalen da suke fuskanta a harkokin kasuwancinsu shi ne zaman fargaba saboda rashin tsaro.

Bayan hauhawar farashen kayayyaki da ke shafar hada-hadar kasuwanci, ‘yan kasuwar sun koka da cewa suna biyan kudin haraji sosai kafin kayansu su isa kasuwa, kasancewar galibi kayan gwari daga arewacin Najeriya ake kaisu yankin.

Saurari cikakken shirin da Lamido Abubakar ya gabatar.

please wait

No media source currently available

0:00 0:09:58 0:00
XS
SM
MD
LG