Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

KASUWA: Hada Hadar Kasuwanci A Wata Kasuwar Duwatsu Masu Daraja Da Ke Birnin Jos, Yuni 12, 2022


Yayin da ake hada hadar sayen kayen masarufi a wata kasuwa a Kano
Yayin da ake hada hadar sayen kayen masarufi a wata kasuwa a Kano

Shirin kasuwa na wannan makon ya leka wata kasuwa da ke tsakiyar birnin Jos a jihar Filato inda ake saye da saida duwatsu masu daraja da ake sarrafawa don yin kayan kawa da kwalliya na mata.

WASHINGTON, DC - Alhaji Mustapha Shehu, ya kwashe shekaru da dama ya na sana’ar saida duwatsu irinsu sapphire a kasuwar. Ya ce sana’ar na taimakawa mutane da yawa kama daga mahaka zuwa masu sarrafa duwatsun.

Farashen duwatsun ya bambanta bisa ga darajarsu. Ana samun duwatsun sapphire ne a garin Antan da ke jihar Filato, da kuma Gombe, Taraba, Nguroje, da sauransu a cewar ‘yan kasuwar.

Sai dai ‘yan kasuwar sun koka akan rashin samun tallafi daga gwamnati.

Saurari cikakken shirin cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:09:59 0:00

XS
SM
MD
LG