Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasuwannin Hannayen Jarin Turai Sun Fuskanci Koma Baya


Kasuwannin Turai sun fuskanci koma baya a yau Litinin, yayin da hada-hada ke cigaba, biyo bayan nasarori da wasu kasuwannin nahiyar Asia suka samu.

Kasuwar FTSE ta birnin London tayi sama ne da abin da bai kai kashi daya ba cikin dari ya zuwa safiyar yau Litinin, yayin da CAC ta Paris da kuma DAX a Frankfurt su kuma suka dan yi kasa da hakan.

Kasuwar Nikkei a Tokyo ta samu bunkasar kashi 1.3 cikin dari ya zuwa karshen wuni, yayin da Sensex ta Mumbai tayi kasa ainun da kashi daya. Hang Seng ta Hong Kong ta samu bunkasa amma bata samu sakiya ba. Haka zalika Composite ta Shanghai da KOSPI ta birnin Seoul suka yi kasa ainun kasa da kashi daya amma TSEC ta Taiwan ta ta tashi da kashi 1.1 cikin dari.

An rufe kasuwar S&P/ASX ta Sydney saboda ranar hutu a kasar Australia.

Kasuwannin mai na cigaba da tashi a yau Litinin, inda ake sayar da gangar danyen mai a Amurka dala 39 da senti 92 tashin da ya kai kusan kashi daya cikin dari sannan ana sayar da danyen man kasa da kasa dala 42 da santi 75 ganga guda karin da ya kai kashi daya cikin dari.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG