Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasuwar Hatsi a Damaturu ta Farfado


Alhaji Ibrahim Geidam gwamnan jihar Yobe
Alhaji Ibrahim Geidam gwamnan jihar Yobe

Shekaru biyu da suka wuce lokacin da hare-haren Boko Haram suka yi tsanani a jihar Yobe kasuwar hatsin dake Damaturu kusan mutuwa ta yi amma yau ta farfado sabili da kwanciyar hankali a jihar Yobe.

Bangarorin kasuwanci da ilimi sun samu koma baya a jihohin arewa maso gabas musamman jihohi ukun dake cikin dokar ta baci wato Adamawa, Borno, da Yobe inda a wasu lokuta harkokin kasuwanci suka tsaya.

A jihar Yobe kasuwar hatsi ta Damaturu ta kusa ta mutu cikin shekaru biyu da suka gabata sabili da tashin tashinar 'yan kungiyar Boko Haram.

Kasuwar Damaturu tana ci ne kowace ranar Lahadi. Wakiliyar Muryar Amurka Sa'adatu Fawu ta leka domin ta gani da idanunta lamuran dake faruwa a kasuwar. Ta leka yankin masu sayarda hatsi inda ta zanta da Alhaji Kali Bukar wani shugaban masu sana'ar sayar da hatsi. Yace kasuwar ta koma kamar yadda take da can. Yanzu za'a ce ma ba'a taba tashin hankali a kasuwar ba. Ana kawo kaya daga koina kuma masu saye na zuwa daga wurare daban daban har ma daga Kano. Yanzu kasuwar ta kankama to saidai akwai karancin kudi.

Kodayake a yankin Damaturu ba'a samu an yi noma sosai ba amma kudancin jihar an yi noma dalili ke nan hatsi ya wadata.

Ga karin bayani.
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:51 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG