Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hankali Ya Kwanta a Iga


Hanyar zuwa Lafia daga cikin garin Akwanga, Jihar Nassarawa.
Hanyar zuwa Lafia daga cikin garin Akwanga, Jihar Nassarawa.

Yanku kura ta lafa a rigimar da ta jawo asarar rayuka da dukiyoyi a Iga dake jihar Nassarawa.

Rundunar ‘yan sandan jihar Nassarawa, ta tabbatar da yanyin kwanciyar hankali a garin Iga dake karamar hukumar Nassarawa Egon, bayan wani tashin hankalin da yayi sanadin rasa rayuka da dukiyoyi da dama a karshen makonnan.

Kakakin rundunar ‘yan sandan a Jihar Nassarawa, ASP Umar Isma’ila ya tabbatar da aukuwar lamarin, kuma yace yanzu haka ‘yan sanda na binciken wanda ya haddasa aukuwar lamarin, da niyyar hukunta su.

“To mu dai ya zuwa yanzu, gawarwakin da muke da su, guda biyar ne, wadanda mun kaisu mutuwari a asibiti”, a cewar ASP Isma’ila.

Mr. Isma’ila ya bayyana matakan da suke dauka a halin yanzu domin tabbatarwa zaman lafiya ya tabbata a Iga “an tura jami’an tsaro wajen, kuma tun a lokacin an samu kwanciyar hankali a wajen, kuma inshaAllahu wadanda sukayi wannan abu zamu tabbatar an kama su an hukunta su.”

Shugaban matasan kabilar Egon ya gargadi matasa akan su daina daukar doka a hannunsu, sai dai su ringa shaidawa shugabanninsu duk wani lamari da ya auku.
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:34 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG