Accessibility links

An nadawa kasuwar dabbobi ta kasa da kasa dake Lesha Barba jihar Kwara sabon sarki.

Alhaji Muhammed Oro Kamba aka nada domin ya jagoranci kasuwar.

Bayan nadin wakilin Muryar Amurka ya tambayeshi abun da zai fi mayarda hankali akai. Sai yace abun da zai sa gaba shi ne gujewa hainci. Yace kamar yadda Allah ya sa suka zabeshi shugabansu su rikeshi da kyau shi kuma ya rikesu da kyau. Babu nuna banbanci ko kabilanci. Babu batun bayerabe ko bashaushe ko kuma wata kabila. Zai rike kowa. Yadda Allah ya hadasu su zauna lafiya. Babu cin amana.

Alhaji Kamba yace abun da yasa mutane suka taru har suka zabeshi sun sanshi da adalci da tsare gaskiya. Shi baya cin amanar jama'a kuma baya yiwa kowa zalunci.

Sarkin Filanin Lesha Barba yace shi ne ya fi kowa farin ciki domin an yi lafiya an kuma tashi lafiya. Jama'ar da suka kasance sun sa kamar yayi kuma domin wadanda shi bai sani ba sun halarci nadin.

Shi ma sarkin Hausawan Lesha Barba cewa yayi nadin yayi masa dadi kwarai. Yace sun tara taro shi kuma wanda aka nada ana sonshi.

Wani daga Jamhuriyar Niger yace ya zo nadin sarkin ne tun daga kasarsa. Yace nadin yayi kyau kuma an yiwa sarkin alheri. Akwai wasu ma da suka fito daga kasar Mali kuma sun yaba da nadin.

Ga rahoton Hassan Umaru Tambuwal.

XS
SM
MD
LG