Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Daruruwan Mutane na ta Gudu Daga Arewacin Jahar Adamawa


Jama'a na ta gudu daga gidajen su saboda rikicin Boko Haram.

Mutanen su na gudu ne saboda karon karfen battar da ake yi tsakanin sojoji da 'yan Boko Haram.

Daruruwan mutane na ci gaba da yin tururuwa su na ficewa daga wasu sassan arewacin jahar Adamawa kamar su Madagali, da Michika da Gulak da Bazza da kuma Mubi bayan fafatawar da ake yi tsakanin sojojin Najeriya da 'yan Boko Haram wadanda suka kama wasu wurare har ma suka kakkafa tutocin su.

Bayanai sun tabbatar da cewa An fitar da Sarkin Mubi daga garin a daidai lokacin da ake kyautata cewa 'yan Boko Haram din zasu darkaki garin na Mubi.

Haka kuma bayanai sun tabbatar da cewa a fafatawar da sojojin Najeriya suka yi da 'yan Boko Haram a garin Bazza tsautsayi ya rutsa da dan tsohon shugaban kasar Najeriya, Laftana-Kanal Adeboye Obasanjo wanda ke shugabantar rundunar sojojin.

Wakilin Sashen Hausa a jahar Adamawa Ibrahim Abdulaziz ne ya aiko da rahoton.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:30 0:00
Shiga Kai Tsaye

Zauren VOA Hausa #EndSARS

Zauren VOA Hausa #EndSARS Kashi na Biyu 03
please wait

No media source currently available

0:00 0:18:31 0:00
Karin bayani akan #ENDSARS: Zanga Zangar Kyamar Gallazawa Al’umma Da Yan Sanda Ke Yi

Rayuwar Birni

Hira da Yusuf, wani dan asalin Jamhuriyar Nijar da ya shekara a Abuja yana sana’r gyaran takalmi
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:39 0:00
XS
SM
MD
LG