Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Katse Hanyar Sadarwa Ya Jefa Wasu Cikin Halin Ihunka-banza A Najeriya


Taron Masu Ruwa Da Tsaki Kan Tsaro a Sokoto
Taron Masu Ruwa Da Tsaki Kan Tsaro a Sokoto

A Najeriya matakan da wasu jihohin suka dauka na kawo karshen ayukkan ta'addanci, musamman katse hanyar sadarwa na ci gaba da jefa jama'a cikin halin Ihun-ka-banza domin ‘yan bindiga na ci gaba da addabar su ba tare da ana jin kukan su ba.

Yanzu haka al'ummomi a wasu jihohin arewacin Najeriya na cikin yanayin dokokin da gwamnatocin su suka dauka don kawo karshen ‘yan fashin daji koda za a samu sauki ga matsalolin da suke haifarwa, ciki har da katse hanyoyin sadarwa.

Wannan yanayin dai bai hana ‘yan fashin dajin ci gaba da kai farmaki ga jama'a ba duk da yake wadannan dokokin suna shafar su.

A jihar Sokoto dake arewa Maso yammacin Najeriya, irin haka na ta faruwa kamar yadda barayin suka shiga yankin Gudu dake arewacin jihar suka sace wata matar aure, su kuwa ‘yan banga suka bi sawunsu cikin daji inda har aka zubar da jini.

A yankin Goronyo ma bayanai sun nuna ‘yan bindigar sun shiga yankin suna harbin kan mai uwa da wabi, inda suka hallaka mutane akalla hudu.

Wakilin sashen Hausa na Muryar Amurka ya nemi jin ta bakin rundunar 'yan sandan Najeriya ta bakin kakakin ta a Sokoto ASP Sanusi Abubakar, amma dai ya ce babu wani bayani a hukumance.

‘Yan Najeriya na ci gaba da mamakin daukar matakan da ake yi amma kuma ba a yi wata azama ba ta farautar barayin, domin matakan kadai ba zasu kawo sauki da kan su ba dole sai an motsa, a cewar Bashir Altine Guyawa shugaban rundunar adalci a jihar Sokoto.

A jihar Kebbi ma yankin Bena dake masarautar Zuru, matakan da aka dauka suna ci gaba da ta'azzarar da lamurran rayuwa acewar wasu mazauna yankin.

Dama dai masu sharhi akan lamurran yau da kullum musamman akan harkar sun bayar da shawarar cewa kamata yi wadannan matakan da ake dauka su kasance na wani Dan lokaci domin idan suka tsawaita sukan iya haifar da wasu matsaloli na daban.

Domin karin bayani saurari rahotan Muhammad Nasir.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:18 0:00


Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG