Hakan na nufin dan wasan na Najeriya, zai zauna tare da jaruman filin wasa na King Power har zuwa 2024 a gasar Premier ta Ingila.
Tsawaita wannan yarjejeniya, na zuwa ne bayan da aka karrama Iheanacho da lambar yabo, saboda ya ci kwallo bakwai cikin wasa hudu da ya buga a gasa daban-daban a kasar ta Ingila.
Dan wasan ya samu lambar yabon ne a matsayin wanda ya fi fice a watan Maris a gasar ta Premier.
“Ina mai matukar farin ciki da aka ayyana ni a matsayin dan wasan da ya fi fice a watan Maris.” Iheanacho ya wallafa a shafinsa na Instagram.
Ya kara da cewa, “Ina godiya ga kungiyar Leicester, abokan wasana, manajan kungiyar, ma’aikata da duk sauran wadanda ke wannan kungiya da kuma masoyanta.”
A shekarar 2017 Iheanacho ya je kungiyar ta Leicester, ya kuma zura kwallo 32 cikin wasa 117 da ya buga mata a iya zamansa da kungiyar.