Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

KENYA: 'Yan Takara 8 Da Suka Fafata A Zaben Da Ya Gabata Za Su Sake Tsayawa


Hukumar zaben kasar Kenya ta fada yau Laraba cewa duk mutane 8 da suka tsaya takara a zaben da aka yi a watan Agusta wanda daga baya kotun kolin kasar ta soke zasu sake tsayawa a zaben da aka shirya yi ranar 26 ga watan Oktoba.

Wata sanarwa daga hukumar zaben, da ake kira IEBC a takaice ta ce, har yanzu dan takarar babbar jam’iyyar adawa Raila Odinga na kan takardar zabe tunda bai bada wasikar janyewa daga zaben ba a hukumance, duk da cewa ya sanarda niyyar yin hakan jiya Talata.

Dubban masu zanga-zanga sun dunguma kan tituna yau laraba a birnin Nairobi, kwana daya bayan da Odinga ya sanar da cewa ba zai tsaya zaben fidda gwanin ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG