Accessibility links

Kirista na hidimar "Lahadin Ganyen Dabino"

  • Ibrahim Garba

Bukukuwan "Ranar Ganyen Dabino" a Birnin Kudus

Kirista a fadin duniya na hidimar Palm Sunday

Kirista a fadin duniya na hidimar Palm Sunday (ko Lahadin Ganyen Dabino).

Dinbin masu ziyarar aikin ibada dauke da ganyayen dabino sun fara hidimar ce da addu’ar jam’I a Majami’ar Sepulcher mai Tsarki da ke Birnin Kudis.

Lahadin Ganyen Dabino dai rana ce ta tuna shigar da Yesu Almasihu ya yi cikin Birnin Kudis cikin nasara, kamar yadda aka rubuta cikin Bisharun farko guda 4 na Linjilar Littafi Mai Tsarki na Kirista.

Lahadin Ganyen Dabinon dais hi ne farkon Mako Mai Tsarki, wanda zai kammalu da hidimar Easter ranar Lahadi mai zuwa.

XS
SM
MD
LG