Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kiristocin garin Sadad suna hijirar gudun ISIS


ISIS
ISIS

Kiristoci da dama da iyalansu sun yi kaura daga daya daga biranen Syria don gujewa abin da ka iya faruwa, kamar yadda masu fafutuka suka fada a jiya Asabar.

Daraktan Kungiyar Kiristocin Syria game da ‘yancin bil’adama, Osama Edward ma ya sanar da cewa, daruruwan Kiristocin da iyalansu ne, suka bar cikin kwaryar garin Sadad zuwa garin Homs da kuma Damascus babban birnin Syria dake karkashin ikon gwamnati.

Sun yi hijirar ne saboda gujewa abin da ka je ya dawo musu, ganin yadda ‘yan kungiyar ISIS ke ta dada kunno kai, zuwa garuruwan da suke da niyyar kai muggan hare-hare. Edward yace, da yawa suna tsoron kar abin da ya faru, na kisan gillar da aka yiwa Kiristocin Kabilar Yazidi ya faru da su.

Kusan kashi 10 daga mutane Miliyan 23 na kabilar Prewar da ke Syria kiristoci ne. Zuwa yanzu dai sojojin taron dangin da Amurka ke jagoranta, sun kai hare-haren sama fiye da sau dubu 6. A jiya 8 ga watan Agustar nan ne, shekara daya cur! da kaddamar da yakar ‘yan kungiyar ta ISIS.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG