Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ko Mene ne Ya Faru a Funtuwa?


Matasa na wasan Fives a jihar Katsina.

​Sai ‘Yan sanda a garin Funtua dake jihar Katsina a arewacin Najeriya, suka yi amfani da borkonon tsohuwa sannan suka samu nasarar tarwasa dalibai masu zanga zanga saboda wasu tambayoyi da suka ce na sabo ne akayi musu a jarrabawa.

Rikicin ya samo asali ne jiya Litinin, sakamakon takardar tambayoyi ta jarrabawar Ingilishi, a aji uku dake babban makarantar sakandare ta Ideal International School, Funtuwa.

Makarantar da ba ta gwamnati ba, itace mafi girma a garin Funtuwa.

Tambayoyi biyu ne a jarrabawar suka harzuka jama’ar garin, wadanda suke zaton batanci ne ga Annabi Muhammad S.A.W.

Wannan shine yasa suka yi zanga-zanga da yunkurin kona makarantar da ma wasu wuraren ibada.

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta tabbatar da aukuwar lamarin, kamar yadda kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, D.S.P Aminu Sadiq yayi bayani.

D.S.P Sadiq yace “wadannan tambayoyi guda biyu, wasu malamai suna gani kamar cin zarafi ne ga Annabi (S.A.W), wannan shine ya sa suka hade kansu, suka je zasu kona wannan ita makaranta”.

“Bayan rundunar ‘yan sanda ta jihar Katsina ta samu wannan rahoto, sai ta tura jami’an tsaro a tabbatar da cewa an kwantar da hakali”, a cewar D.S.P Sadiq.

Mr. Sadiq ya kara da cewa “bayan wuta ta lafa, sai su samari suka sake hade kansu, sai suka zagaya suka sami wani Coci mai suna Catholic Church, suka saka ma kujerun wuta, kuma sai suka zagaya, ita wannan makarantar baya, sai suka saka wuta, a halin yanzu akwai block da rufinsa ya kone. Babu mutuwa babu rauni, anyi amfani da jami’an tsaro da borkonon tsohuwa wajen tarwatsasu.

Yanzu haka dai kura ta lafa a garin, to amma wasu rahotanni na cewa ana zaman dar-dar, abunda kennan ya sa aka baza jami’an ‘yan sanda da sojoji a dukannin titunan garin.

Ita kuma gwamnatin jihar Katsina ta bada umarnin rufe makarantar nan take, tare da yin kashedi ga jama’a akan daukar doka a hannunsu, inda kuma ta sha alwashin gudanar da bincike da ladabtar da duk wanda aka samu da hannu a cikin lamarin.
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:16 0:00
Shiga Kai Tsaye

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG