Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Komai Tsit A Bakin Iyakar Sham Da Turkiyya


Sojojin Turkiyya cikin tankar yaki a bakin iyakar kasar da Sham, Jumma'a 5 Oktoba 2012

Sojojin Turkiyya su na sintiri a bakin iyakar kasar da Sham, bayan musanyar wuta da kasashen biyu suka yi cikin wannan makon.

Sojojin Turkiyya su na yin sintiri yau Jumma'a a bakin iyakar kasar da Sham, a bayan wani mummunan hari a wannan makon.

Dakarun na Turkiyya sun fara wannan sintiri a bayan da suka yi luguden wuta kan wasu sassan kasar Sham, kuma a bayan da majalisar dokokin Turkiyya ta bayar da iznin daukar matakan soja a wajen kasar idan har bukatar haka ta taso.

Turkiyya ta yi luguden wutar a bayan wani harin da aka kai da makamai masu cilla kwanson bam daga tsallaken iyaka zuwa kan garin Akcakale na Turkiyya a ranar laraba, har aka kashe fararen hula 5.

Jiya alhamis, Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya yayi tur da harin da aka kai kan Akcakale, daya daga cikin al'amura mafiya tsanani da aka gani cikin watanni 18 da fara yin tunzuri a kasar Sham.

Kwamitin Sulhun ya ce wannan lamarin ya nuna irin mummunar illar da rikicin kasar Sham ke yi kan tsaron makwabtanta da kuma zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.

Firayim ministan Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, yace kasarsa ba ta da niyyar tayar da yaki, amma kuma ta kuduri aniyar kare iyakokinta da kuma al'ummarta.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG