Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rasha Ta Shiga Yakin Syria da Zummar Kare Gwamnatin Al-Assad


Shugaban Bashar al-Assad

Yanz da a fili take cewa Rasha ta shiga yakin Syria da nufi kare gwamnatin Bashir Al-Assad

Wani kusa, a wakilan majalisar dokokin Rasha yace sai ta yiwu wata "rundunar sojojin sakai" ciki harda rikakku daga fagen dagar da ake yi a gabashin Ukraine,zasu shiga sahun sojojin Syria a fafatawar da dakarun suke yi da mayakan sakai na ISIS da wasu kungiyoyin ta'adanci a Sham din.

Admiral Vladimir Komoyedov, a magana d a yayi da kamfanin dullancin labarai na Rasha da ake kira Interfax jiya Litinin yace da "alamu" sojojin Rasha zasu shiga yakin da ake yi a Syrian. Sai dai Komoyedov bai bada wani jadawali na sa'ar da sojojin zasu shiga yakin ba,kuma zuwa yanzu fadar Kremlin da shugaban Rasha basu ce komi akan kalaman nasa ba.

Furucin dan majalisar dokokin yana zaman martani ne ga rahotannin da ba'a tabbatar ba cewa an ga "mayakan sakai na Rasha" a fagen daga suna aiki da sojojin Syria.

A gefe daya kuma, kungiyar tsaro ta NATO ta nemi Rasha ta yi mata bayani, bayan da hukumomin Turkiyya suka bada rahotannin cewa jiragen yakin Rasha sun yi kutse cikin kwanaki biyu da suka wuce cikin aewacin Turkiya, cewa suna auna muradun 'ya 'yan ta'adda ne. Wani babban jami'in a Moscow ya aza laifin kan rashin kyawun yanayi a zaman dalilin da ya janyo hakan.

A makon jiya ne Rasha ta fara kai farmaki da jiragen yaki a Syria, kan abunda take ikirarin cewa tana kai hari kan kungiyar ISIS, da wasu kungiyoyin 'yan ta'adda-watau kungiyoyin 'yan tawayen Syria wadanda basa goyon bayan gwamnatin kasar.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG