Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Koriya Ta Arewa Ta Gargadi Amurka


Shugaba Kim Jong Un
Shugaba Kim Jong Un

Shugaban Korea ta arewa ya bayyana cewa a shirye kasar sa take da ta saki makamin nukiliya a kowanne lokaci.

Shugaban kasar Korea ta Arewa Kim Jong Un ya ce dole ne Amurka ta yarda cewa shirin Nukiliyar kasarsa na zahiri ne.

A cikin jawabinsa na Sabuwar Shekara a yau litinin, Kim yayi gargadin cewa yana da makunnin Nukiliya a kan teburinsa. Shugaba Kim yace, "makamanmu na nukiliya zasu iya kaiwa ko ina a cikin Amjurka. Amurka ba zata iya abka min, ko kuma kasar mu da yaki ba."

Shugaban na Koriya ta Arewa yace kasarsa, zata iya "jure ma kowace irin barazanar nukiliya daga Amurka, kuma tana da rigakafin nukiliya da zai iya hana Amurka yin wasa da wuta."

Yace tilas Amurka ta gane cewa wannan abu na zahiri ne, ba wai kawai barazana ce be. Ana daukar jawabin Sabuwar Shekara da Kim Jong Un yake yi a zaman mai nuna manufa da kuma inda kasarsa ta dosa a cikin sabuwar shekara.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG