Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Koriya Ta Arewa Ta Yi Barazanar Janyewa Daga Taron Kolin Trump Da Kim


Shugaba Kim da Shugaba Trump
Shugaba Kim da Shugaba Trump

Korea ta Arewa ta yi wata barazanar farat daya cewa, zata janye daga taron koli da Amurka kana kuma tana bayyana shakkunta a kan dakatar da shirinta na nukilya.

Shugaban Korea ta Arewa Kin Jong Un ya amince ya gana da shugaban Amurka Donald Trump a ranar 12 ga watan Yuni a kasar Singapore, domin kulla yarjejeniyar da zata kawo karshen shirin nukiliyar Korea ta Arewa inda ita kuma Amurka zata tabbatar mata da tsaro da kawo karshen jan kunne na takunkuman tattalin arziki.


Amma a yau Laraba karamin ministan harkokin wajen Korea ta Arewa Kim Kye Kwan ya fitar da wata sanarwa ta kamfannin dillancin labaran kasar KCNA dake sukar kalamai marasa lizzami da mai baiwa shugaban Amurka shawara a kan tsaro John Bolton ya yi cewa Pyongyang ta wargaza baki dayan makamanta na nukiliya da na makamai masu lizzami da masu guba kafin ta samu wata diya ko tabbatar da bukatunta.

Ministan ya bayyana takaicinsa ga matsayar da Amurka ta dauka kuma yace akwai yiwuwar Korea ta Arewa zata janye daga taron kolin Trump da Kim, har sai gwamnatin Trump ta tabbatar da adalci wurin inganta dagantakarsu ta hanyar tattaunawa.


Kalaman na karamin ministan harkokin wajen na zuwa ne jim kadan bayan Arewar ta soke kai tsaye wata tattaunawar yau Laraba, yana nuni da atisayin sojoji na hadin gwiwa tsakanin Amurka da Korea ta Kudu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG