Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Koriya ta Arewa Tayi Brazanar Yanke Hanyar Tattaunawa da Amurka


Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un
Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un

A wani matakin mayar da martani bisa takunkumin da Amurka ta kakabawa shugaban kasar Koriya ta Arewa, Kim Jong Un, kasar tayi barazanar yanke duk wata hanyar tattaunawa tsakaninsu.

Kasar Korea ta Arewa ta ce za ta rufe wata kafar ganawa ta karshe da kasar Amurka, a matsayin martani ga matakan da hukumomin Washington su ka dauka na kakaba takunkumi akan shugabanta Kim Jong Un da ake zargi da aikata laifukan cin zarafin bil adama.

A yau Litinin hukumomin Pyongyong sun gayawa Amurka cewa kasar za ta yanke duk wata huldar diplomasiyya da hukumomin Washington da ke gudana, ta ofisoshinta da ke hedkwatar Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York.

A makon da ya gabata, Amurka ta kakaba takunkumi akan shugaba Kim da wasu jami’an Korea ta arewan, baya ga wasu jerin takunkumi da aka sakawa kasar a baya, saboda shirinta na mallakar makamshin nukiliya.

Da safiyar Litinin kuma Korea ta arewar ta yi barazanar daukan wani mataki akan Amurka da hukomomin Seoul, bayan da suka ayyana shirinsu na tura makaman kariya daga makamai masu linzami zuwa Korea ta kudu.

Pyongyong ta yi wannan barazanar ce kwanaki da dama suka gabata, bayan da Washington da Seoul suka ayyana shirin yin amfani da wani nau’in makamin kariya kirar THAAD a yankin ruwan Korea, bayan gwaje-gwajen makamai masu linzami kirar Ballistic da hukumomin Pyongyong suka yi.

XS
SM
MD
LG