Koriya ta Arewa, ta bukaci cewar kada Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Mike Pompeo, ya sake shiga tattaunawar da ta shafi ayyukanta na nukiliya.
Kwon Jong Gun, wani babban jami'in ma'aikatar harkokin wajen Koriya ta Arewa, ya ce Pyongyang ta na son wanda ya kasance "mai hankali da kuma iya Magana cikin mutuntawa", a cewar wani rahoto daga jami'an kamfanin dillancin labarai na Koriya ta Arewa-KCNA.
Wannan kalaman na Kwon Jong Gun, sun fito sa’o’i bayan da gwamnatin ta kaddamar da wani sabon shirrin gwajin makami mai linzami wanda suka kira "jigon dabarar makamai," wanda ya nuna karfin sojojin na Pyongyang.
Kamfanin dillancin labarai na KCNA, ya ce Kim Jong Un, ya jagoranci gwaje-gwajen jiya Laraba, ya kuma kira shi "aiki mai mahimmanci."
Za ku iya son wannan ma
-
Fabrairu 08, 2023
An Kama Wani Likitan Da Ya Yada Cutar Sankarau A Mexico
-
Fabrairu 06, 2023
Wata Girgizar Kasa Ta Kashe Mutane Akalla 5,000 A Turkiyya Da Siriya
-
Fabrairu 04, 2023
Amurka Ta Kakkabo Babban Balan-Balan Na Leken Asirin China
-
Janairu 31, 2023
Fafaroma Francis Ya Kai Sakon Zaman Lafiya A Afirka Ta Tsakiya
-
Janairu 30, 2023
Mutane 88 Sun Mutu A Wani Harin Bomb A Pakistan
Facebook Forum