Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomin Koriya Ta Kudu Sun Kai Ziyara Koriya Ta Arewa


Tawagar 'yan Koriya a yayin da suke tattaunawa
Tawagar 'yan Koriya a yayin da suke tattaunawa

Jakadu na musamman daga shugaban kasar Moon Jae-in, sun gana da shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un a yau litinin, har shugaban na Koriya ta rewa ya shirya wa bakin zaman cin abincin dare.

Tawagar mai mutane goma karkashin jagorancin babban mai bada shawara kan tsaro ga Shugaba Moon, mai suna Chung Eui-Yong, sun isa Pyongyang kai tsaye daga birnin Seoul wanda ba kasafai hakan ke faruwa ba; domin isar da sakon Moon dangane janye makaman Nukiliya daga yankin , da kuma samun dawwamammen zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin baki daya.
A yayin da yake Magana da manema labarai kafin ya kama hanya, Chung yace zai isar da sakon shugaba Moon wnada ya kunshi kudiri da kuma niyyar ganin an kwance damarar makaman Nukiliya da kuma tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali mai dorewa a yankunan Koriyar biyu.
Haka nan Chung yace, zai yi iya kokarin shi domin yaga cewa sun tattauna sosai da nufin samo hanyar da za’a farfado da shawarwari tsakanin Pyongyand da hukumomin Amurka dake Washington.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG