Musabbabin sa irin wadannan tufafin shi ne kare kai daga cutar zika da sauro ke yadawa, wanda kan haddasa dan radadi kawai ga wasu mutane, amma kuma kan haddasa haihuwar nakasasshen jariri muddun uwa na dauke da cutar.
An kuma gano cewa cutar na yaduwa ta hanyar jima'i, wanda ke nuna cewa idan 'yar wasu ta kamu yayin da ba ta da ciki, ta na iya kawo cutar gida ta yada ta ga mijinta.