Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Ta Bada Belin Tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele Bayan Shafe Kwanaki 151 A Tsare


Godwin Emefiele (Hoto: Facebook/CBN)
Godwin Emefiele (Hoto: Facebook/CBN)

A wani muhimmin mataki da wata babbar kotun babban birnin tarayya Abuja ta yanke yau Laraba a Maitama, Kotun ta bayar da belin tsohon gwamnan babban bankin Najeriya Godwin Emefiele bayan shafe watanni biyar da kwanaki a tsare.

Mai shari’a Olukayode Adeniyi, wanda ya jagoranci shari’ar, ya jaddada wajibcin bin doka da oda da kuma tabbatar da adalci ga wadanda ake tuhuma.
Emefiele, wanda ke hannun jami’an tsaro na gwamnati tun ranar 9 ga watan Yuni, an sake shi ne biyo bayan wata takaddamar shari’a da ta hada da gwamnatin tarayya, da babban lauyan gwamnatin tarayya, da kuma hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC.

Hedkwatar Hukumar EFCC Da Ke Abuja
Hedkwatar Hukumar EFCC Da Ke Abuja

Kotun ta yi la’akari da tanade-tanaden kundin tsarin mulkin Najeriya da kuma kammala binciken tuhume-tuhumen da ake yi wa tsohon shugaban babban bankin na CBN tun a watan Agustan bana, ta ce dole ne a daina tsare wanda ake tuhuma ba tare da an gurfanar da su a gaban kotu ba.

Mai shari’a Adeniyi ya jaddada muhimmancin kiyaye hakkin dan Adam na wadanda ake tuhuma, yana mai jaddada cewa lokacin da aka shafe ana tsare da tsohon gwamnan babban bankin na Najeriya ya wuce abin da doka ta tanada.

Lauyan Emefiele, Matthew Burkaa (SAN), ya yi nasarar bayar da hujjar a saki wanda yake karewa, inda ya karyata rade-radin da ake yi na yin katsalandan ga shari’ar da ke tafe.

Haka zalika, an umurci tsohon Gwamnan na CBN ya ajiye dukkan takardun tafiyarsa na fasfo a gaban magatakardar kotun, har sai an ci gaba da shari’a. Wannan mataki dai ya na nuni da kokarin kotun wajen ganin samun daidaito tsakanin girmama ‘yanci dan Adam da kuma bin tsarin doka da oda wajen bincike da tabbatar da adalci ga dukkan bangarori.

Emefiele ya fara jan ragamar babban banki na CBN ne a shekara ta 2014, sakamakon dakatar da Sanusi Lamido Sanusi sarkin kano na 14.
A zamanin Emefiele, an sami canje-canje da sauye sauye da suka janyo cece-kuce a Najeriya inda aka sami ra’ayoyi maban banta da dama a wancan lokaci, musamman ga lamarin da ya shafi sauya fasalin kudin kasar wanda aka aiwatar a watan Oktoban 2022.
Emefiele, ya sauya fasalin kudin Najeriya da ya hada da naira dubu, dariya biyar da dari biyu da niyyar magance matsalolin da suka shafi maganin masu garkuwa da mutane da karbar kudin fansa, rage zirga-zirgan kudin takardar da zummar karawa naira daraja.
Sai dai matakan sun janyo cece kuce sosai a kasa da jefa jama’ar kasar cikin mawuyacin hali, inda ‘yan siyasa da dama ke ganin matakin an dauka ne kurum dan yi musu zagon kasa musamman lura da cewa a wancan lokacin kakar zabe ne.
Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da Emefiele ne a ranar 9 ga watan Yuni inda kwana daya da dakatar da shi, hukumar tsaro ta farin kaya ta DSS ta kama shi kuma ta tsare shi.
Bayan shafe dimbin kwanaki a hanun hukumar DSS, daga baya bayan nan hukumar ta sake shi inda itama hukumar EFCC ta sake cafke shi kuma ta tsare shi a hanunta.
Kamar yadda labarin belin Emefiele ke ci gaba da bayyana, ya zama abin tunatarwa game da daidaito tsakanin jami'an tsaro da kiyaye haƙƙin mutum a cikin yanayin shari'a.
Shari’ar Emefiele ta bayyana bukatar kara nuna gaskiya da bin ka’idojin shari’a ta kasa, tare da jaddada wajabcin kiyaye hakkin wadanda ake tuhuma da kuma tabbatar da cewa an tafiyar da harkokin shari’a cikin gaskiya da adalci.
~ Yusuf Aminu Yusuf

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG