Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Jami'an DSS Suka Sake Kama Emefiele Bayan Wata ‘Yar Hatsaniya


Jami'an tsaro na DSS a Najeriya (Hoto: AP)
Jami'an tsaro na DSS a Najeriya (Hoto: AP)

Hatsaniyar ta kaure ne a lokacin da jami’an gidan yari da na hukumar farin kaya ta DSS suka fara kai ruwa rana kan wanda zai tafi da Emefiele bayan da aka kammala zaman kotun.

Yar hatsaniya ta kaure a farfajiyar kotun tarraya da ke birnin Legas a Najeriya bayan da aka ba da belin tsohon gwamnan Babban Bankin kasar Godwin Emefiele.

A ranar Talata alkali Nicholas Oweibo, ya ba da belin Emefiele akan Naira miliyan 20 da kawo wani mutum da zai biya adadin hakan kafin a ba da belinsa.

Ya kuma ba da da umurnin a ci gaba da tsare shi har sai ya cika sharuddan, wadanda suka hada har da mika fasfo dinsa.

Sai dai hatsinya ta kaure a wajen kotun a lokacin da jami’an gidan yari da na hukumar farin kaya ta DSS suka fara kai ruwa rana kan wanda zai tafi da Emefiele.

Bayanai sun yi nuni da cewa jami’an na DSS ne suka tafi da shi a karshe bayan da hatsaniyar ta kai ga yaga rigar daya daga cikin jami’an gidan yarin.

Tun a watan Yuni Emefiele yake tsare a hannun DSS har zuwa ranar Talata da aka gurfanar da shi a kotu.

Ana tuhumar Emefiele da laifin mallakar makamai, zargin da yake musantawa.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG