Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Ta Haramtawa Secondus Bayyana Kansa A Matsayin Shugaban PDP


Uche Secondus (Instagram/ Uche Secondus)

Ibeawuchi Ernest Alex, Dennis Nna Amadi, Emmanuel Stephen da Umezirike Onucha, wadanda kusoshi ne a jam’iyyar ta PDP suka shigar da karar.

Wata kotu a jihar Rivers da ke kudu maso kudancin Najeriya, ta hana Uche Secondus ya rika ayyana kansa a matsayin shugaban jam’iyyar PDP.

Matakin kotun na zuwa ne yayin da ake ci gaba da takaddamar cikin a babbar jam’iyyar adawar ta PDP inda wasu jigajigan jam’iyyar ke neman Secondus ya sauka da mukaminsa yayin da shi kuma ya yi kememe ya ki sauka.

A ranar Litinin Mai Alkali O. Gbasam ya zartar da hukuncin a wata kara da aka shigar da Secondus kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Kotun ta kuma dakatar da shi daga gudanar da taron kananan hukumomi da na mazabu har sai an kammala sauraren karar.

Uche Secondus (Facebook/ PDP)
Uche Secondus (Facebook/ PDP)

Ibeawuchi Ernest Alex, Dennis Nna Amadi, Emmanuel Stephen da Umezirike Onucha, wadanda kusoshi ne a jam’iyyar ta PDP suka shigar da PDP da Secondus kara a cewar jaridar Vanguard.

A dai watan Dismbar shekarar 2017 aka zabi Secondus a matsayin shugaban jam’iyyar a babban taron da jam’iyyar ta yi a Abuja.

Hakan na nufin sai a watan Disambar bana wa’adinsa zai kare, amma masu adawa da mulkinsa, wadanda ke zarginsa da wargaza tafiyar jam’iyyar, sun nemi ya sauka daga mukamin, suna masu cewa shi ne musabbabin da ya sa ake ta fita daga jam’iyyar, zargin da Secondus din ya musanta.

Gwamnonin PDP a wani taro da suka yi kwanan nan (Twitter/ PDP)
Gwamnonin PDP a wani taro da suka yi kwanan nan (Twitter/ PDP)

Rahotanni baya-bayan sun ce an ba Secondus zabin ya shirya babban zaben jam’iyyar a watan Oktoba mai zuwa, amma ya yaki, yana mai cewa sai ya kammala wa’adinsa kafin ya sauka.

A ‘yan makwannin da suka gabata ne wani taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar ta PDP da aka fadada a Abuja, ya yanke shawarar katse wa’adin mulkin Secondus a watan Oktoba domin neman mafita ga rikicin cikin gida da ya ki ci ya ki cinyewa a jam’iyyar.

XS
SM
MD
LG