Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Ta Sake Watsi Da Umurnin Trump Na Hana Shiga Amurka


Shugaban Amurka Donald Trump wanda ya kafa dokar hana mutanen wasu kasashen musulmai shida shigowa kasarsa.
Shugaban Amurka Donald Trump wanda ya kafa dokar hana mutanen wasu kasashen musulmai shida shigowa kasarsa.

A karo na biyu wata kotun tarayya a jihar California ta sake haramta wa shugaban Amurka Donald Trump aiwatar da dokar hana mutane daga wasu kasashe shida na musulmi shigo wa Amurka.

Kotun daukaka kara ta 9 dake San Francisco, ba tare da wata hamayya ba, ta yanke hukuncin jiya litinin akan dokar ta Trump, a bisa dalilin cewa shugaban ya wuce gona da iri wajen amfani da karfin ikonsa da kundin tsarin ya ba shi a lokacin da ya sanyawa dokar hannu ranar 2 ga watan Maris.

Kotun mai alkalai guda uku ta ce yayin da dokar shigi-da-fice ta kasa, ta shekarar 1952 ta ba shugaban kasa ikon sa ido akan masu shiga Amurka da kuma tsaron kasar, “batun shige da fice ba aikin mutum daya bane, koda kuwa shugaban kasa ne.”

Wannan hukuncin na jiya Litinin ya kara karfafa hukuncin da wata kotun daukaka kara ta jihar Virginia ta yanke, wadda ita ma ta goyi bayan hukuncin da wani alkali a jihar Maryland ya yanke na takawa wasu bangarorin dokar burki.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG