Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Ta Tabbatar Da Nasarar Yuweri Musveni A Zaben Uganda


Kotun kolin kasar Uganda ta tabbatar da nasarar da shugaban kasar Yuweri Musveni ya samu a zaben da aka yi ranar 18 ga watan Fabrairu.

Ko kuma ta yi watsi da wani korafi da tsohon Firai ministan kasar kuma dan takarar mukamin shugtaban kasa a zaben, Amama Mbabazi ya shigar.

A ranar 20 ga watan Fabrairu hukumar zaben kasar ta ayyana Musevi a matsayin wanda ya lashe zaben, bayan da ya samu kashi 60 na kuri’un da aka kada, inda abokin hamayyarsa Kizza Besigye ya samu kashi 30.5.

Shi dai Mbabazi ya nemi kotun ta soke zaben bisa dalilan cewa hukumar zaben kasar ba ta bi dokokin zabe ba.

Sai duk da cewa ta amince akwai kura-kurai nan da can da ba a rasa ba, kotun ta ce ba su kai ga a soke zaben ba.

Ministan watsa labaran kasar, Jim Muhwezi ya ce wannan matsaya da kotun ta dauka, ta nuna zabin ‘yan kasar Uganda a lokacin da suka zabi Museveni.

Ya kara da cewa yanzu ya rage ne shugaba Musevi da ‘yan tawaye su hada kansu bayan wannan matsaya da kotun ta dauka.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG