Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masu Fashi Da Makami Sun Addabi Jama'a


'Yan fashi

Jama’a da dama sun rasa rayukansu sanadiyar wannan aika aika na masu fashi da makamai

A ‘yan kwanakin nan masu fashi da makamai sun hana jama’a da makiyaya dake karkara sukuni saboda hare haren da suke kaddamarwa akan al’umar kauyukan.

Jama’a da dama sun rasa rayukansu sanadiyar wannan aika aika na masu fashi da makamai a sassa daban daban a jihar Maradi, wanda hakkan ya sa babban sakatare a fadan Gwamnan Malam Yahaya Godi, ya tabbatarwa muryar Amurka, afkuwar hare haren.

Kasancewar haka kwamitin yaki da daukar makamai ba bisa ka’ida ba ya fara horas da jami’an tsaro na iyakokin Diffa, Maradi Tawa da Zandar, akan makamai da suke aiki dashi da binciken masu dauke da makami babu izini.

Ecowas da tarayyar Turai ne suka dauki nauyin gudanar da horaswan domin kare mutane da dukiyoyinsu kuma a tabbatar da zaman lafiya a cikin kasashen.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:37 0:00

An Ga Watan Azumi A Najeriya - Sultan

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammada Sa'ad Abubakar Ya Ba Da Sanrwar Ganin Watan Ramadan
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
Wani Sirri Da Tsohon Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou Ya Fadawa ‘Sarki Sanusi II’
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:23 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

An Kai Wa Ofisoshin Kungiyar Ba Da Agaji Hari A Arewa Maso Gabashin Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:02 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG