Jiya Talata, lauyoyin gwamnatin tarayya da na jihohin Washington da Minnesota, wadanda suka shigar da karar don neman a hana aiki da dokar, suka gabatar da hujjoji a gaban kwamitin alkalai uku.
Lauyan gwamnatin tarayya August Flentje, yace dokar da shugaba Trump ya kafa tayi dai dai da huruminsa kamar yadda majalisar dokoki da tsarin mulkin Amurka suka tanadar.
Da yake amsa tambayoyin alkalan kan yadda dokar tayi illa ga jahar Washington, Noah Purcell, yace dokar ta raba iyalai,kuma ta sa dalibai da suke shirin dawowa Amurka makalewa a ketare,wanda ya jefa mutane cikin rashin tabbas kan ko suyi balaguro ko kuma a'a.
Da alkalan suka kalubalance shi kan cewa ko dokar ta nunawa musulmi wariya,ganin akwai musulmin da dokar bata shafesu ba, Purcell yace ba sai dokar ta shafi dukkan musulmi ba kamin a gane ta sabawa tsarin mulki ba.
Atoni Janar na jihohin Amurka 15 sun gabatar da bayanai ga kotun na goyon baya ga jihohin Minnesota da Washington. Haka nan kamfanoni kusan 100 sun gabatar da matsayarsu na adawa da wannan doka.
Ahalinda ake ciki kuma, ministan tsaron gida na Amurka John kelly, ya gayawa majalisar dokokin Amurka cewa ganin abunda ya faru ya sa ya jinkirta fara aiki da dokar shugaban kasar.
Kelly ya bayyana haka ne lokacinda ya bayyana gaban kwamitin majalisa a karon farko tun bayan da ya kama aiki.