Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun Koli Ta Tabbatar Da Nasarar Fintiri A Matsayin Gwamnan Adamawa 


Gwamnan Adamawa Fintiri (Facebook/Gwamnatin Adamawa)
Gwamnan Adamawa Fintiri (Facebook/Gwamnatin Adamawa)

​​​​​​​Kotun Koli ta tabbatar da nasarar Ahmadu Fintiri a matsayin gwamnan jihar Adamawa inda mai shari’a John Okoro wanda ya shirya kuma ya karanta hukuncin a ranar Laraba ya yi watsi da karar da ‘yar takarar gwamna a karkashin inuwar jam’iyyar APC, Aisha Dahiru ta shigar.

A yayin da kotun ta yi watsi da karar da Binani ta shigar a bisa rashin cancantar, tawagar masu shari’a biyar karkashin jagorancin Mai Shari’a John Okoro ta bayyana cewa, ayyana Binani a matsayin wacce ta lashe zabe da Kwamishinan Zabe wato REC, Hudu Ari laifi ne kuma wani abu ne na rashin gaskiya.

Mai shari’a Okoro ya kara da cewa, baturen zabe ne kawai ya kamata ya bayyana sakamakon zabe, domin a kaucewa hargitsi da rudani a bisa tanadin dokar zabe, kuma wannan alhakin hakan ko iko ya rataya ne kawai a wuyan baturen zaben.

A ranar 20 ga Maris na shekarar 2023 ne Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Najeriya wato INEC ta ayyana zaben gwamnan Adamawa a matsayin wanda bai kammala ba sakamakon cewa tazarar da ke tsakanin manyan ‘yan takarar biyu bai kai adadin masu kada kuri’a dubu 37 da 16 a rumfunan zabe 69 da aka soke zabe ba, a cewar Mele Lamido.

Idan Ana iya tunawa, baturen zabe na INEC, Mele Lamido, ya bayyana cewa Fintiri ya sami kuri’u dubu 421 da 524 a yayin da Binani ta samu kuri’u dubu 390 da 275.

Biyo bayan ayyana zaben a matsayin wanda bai kammala ba ne hukumar zaben ta sanya ranar 15 ga watan Afrilu domin sake gudanar da zaben.

An sami ce-ce-ku-ce a lokacin tattara sakamakon zaben ne biyo bayan da kwamishinan zabe a jihar Adamawa, Hudu Yunusa-Ari, ya ayyana Binani a matsayin wacce ta lashe zaben ba tare da baturen zabe yana nan ba.

Wannan ce-ce-ku-cen ya tilasta wa Hukumar INEC yin watsi da sanarwar Hudu Ari na bayyana Binani a matsayin wacce ta lashe zaben tare da mika sammacin Hudu zuwa hedikwatarta da ke Abuja, yayin da ake ci gaba da tattara sakamakon zaben.

Sakamakon karshe dai ya nuna cewa Binani ta sami kuri’u dubu 398 da 788, a yayin da ta bayyana Fintiri a matsayin wanda ya lashe zaben da kuri’u dubu 430 da 861.

Haka kuma, bayan zaben, hukumar INEC ta dakatar da Yunusa-Ari, kama tare da mika shi ga ‘yan sanda domin gurfanar da shi a gaban kuliya.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG