Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun Najeriya ta tuhumi wani dan kasar Iran dangane da makaman da aka kama


Makami da aka yi fasa kwaurinsu da jami'ai suka kama a Najeriya. (File Photo)

Kotun Najeriya ta tuhumi wani dan kasar Iran dangane da makaman da aka kama.

Wata kotun Najeriya ta tuhumi wani dan kasar Iran da ‘yan Najeriya uku dangane da makaman da aka kama a tashar jirgin ruwan kasar dake Lagos watan jiya. Ba’iraniyen Azim Adhajani ya bayyana gaban kotun majistire dake birnin tarayya Abuja yau alhamis. Ya dai ki amsa ko musanta aikata laifin da cewa, yana bukatar ofishin jakadancin kasar Iran ya wakilce shi. Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya laburta cewa, ana tuhumar mutumin da kuma wani dan Najeriya da laifin hada baki a yunkurin safarar makaman zuwa kasar Gambia. Wani dan kasar Iran din kuma da ake bukata domin amsa tambayoyi yaki bayyana gaban jami’an Najeriya bisa hujjar kariyar diplomasiya. Bisa ga rahotannin, masu binciken sun hakikanta cewa Irananiyawan biyu membobin kungiyar al-Quds ne, wani bangaren ‘yan boko na dogarawan juyi-juyin halin kasar Iran. ‘Yan Najeriya ukun da aka tuhuma da safarar makaman sun hada da Ali Usman Abbas Jega, da Ali Oroji Wamakko da kuma Mohammed Tukur. Farkon wannan makon, kasar Gambiya ta sanar da katse duk wata huldar diplomasiya da kasar Iran. Gambiya bata bada dalilin daukar wannan matakin ba, sai dai wani tsohon jakaden kasar Gambia a Amurka, Essa Bokarr Sey, yace ya yiwu, shugaba Yahya Jammeh ya dauki wannan matakin ne domin neman nisanta kasar da makaman da aka kama a Lagos.

XS
SM
MD
LG