Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun Tarayya Ta Umarci Dakatar Da Babban Taron Jam’iyyar PDP


PDP

Babbar kotun tarayyar Najeriya ta Abuja ta sanar da dakatar da babban taron da kwamitin riko na PDP ya shirya kudanarwa a Port Harcourt.

Alkali Okon Victor Abang, ya rubuta umarnin dakatar da taron da yayiwa hukumar zabe da ‘yan sanda kwafin umarnin, da barazanar sanya a damke shugabannin kwamitin rikon idan har sun ki bin umarnin kotun.

Musamman sanarwar ta gargadi kalamai da ke fitowa daga ‘yan kwamitin rikon da suka hada da Ben Obi da Dayo Adeyeye, da kotun ke dauka a matsayin isgilanci. Shugaban kwamitin amintattun na PDP Sanata Walid Jibrin, ya fadawa wakilin Muryar Amurka Nasiru Adamu, cewa taron na nan kamar yadda aka tsara. Shi kuma kakakin bangaren Sanata Ali Modu Sheriff, Inuwa Bwala, yace taron ya sabawa doka.

Mataimakin daraktan hulda da jama’a na hukumar zabe Nick Dazan, ya bawa PDP shawara, inda yace “abin da yakamata ayi aje ayi sulhu, a zauna kowa ya fadi menene yake mishi zafi, saboda yawan zuwa kotu ba karamin kudi ake kashewa ba, abu na biyu, ba karamin lokaci ake kashewa ba, na uku ba karamin bacin rai zai biyo bayan kace nace da kuma zuwa kotu ba.”

Tun gabanin wannan hukuncin na Abuja, babbar kotun tarayya ta Port Harcourt ta bayar da hurumin gudanar da babban taron. Abin jira a gani shine shin taron zai gudana kamar yadda aka tsara? Shin hukumar zabe zata halarci taron?

Saurari rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya daga Abuja.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:58 0:00

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG